(ABNA24.com) Iran, ta bakin kakakin gwamnatin kasar, Ali Rabii, ta ce yanzu ya rage ga Amurka game da batun na musayar fursunoni.
M. Rabbi, ya ce akwai wata dama ta yin musayar dukkan fursunoni tsakanin bangarorin biyu saidai ba tare da sharadi ba.
Ya ce an riga an sanar da Amurka da anniyarmu, saidai har yanzu bata ce uffan ba.
Iran, ta ce ta damu matuka da halin da ‘yan kasarta da ake tsare da Amurka ke ciki, wadanda ta ce ba’a kula dasu yadda ya kamata.
A watan Disamba ne Iran, ta sanar cewa a shirye ta ke domin kara musayar wasu fursunoni da Amurka, bayan da suka yi musayar wani ba’amurke da ake tsare da a Iran da kuma wani ba’iraniye da ake tsare da Amurka.
/129
11 Mayu 2020 - 05:45
Lambar labari: 1035577
Mahukuntan Teheran, sun nanata cewa a shirye su ke domin musayar fursunoni da Amurka ba tare da wani sharadi ba.